Sarkin Hausawan Jihar Imo Alhaji Auwal Baba Sa’idu Sulaiman, ya karyata labarin da ke cewa mahukuntan Jihar sun kori wasu ‘yan Arewa daga matsugunan su.
Rahotanni dai sun ce an kori mutanen ne daga natsugunan su da ke unguwar Avu-Junction a birnin Owerri.
Sarkin Hausawan, ya karyata labarin ne yayin zantawa da manema labarai, inda ya ja kunnen mutane cewa a guji yada labarun karya, wadanda za su iya haddasa kyamar juna da rikici a tsakanin al’umma.
Ya ce Unguwa Avu-Junction wuri ne da ya hada kabilu daban-daban, kuma Hausawan da ke zaune a wurin ba su wuce kashi 30 cikin 100 na yawan sauran kabilun ba.
Basaraken ya cigaba da cewa, wuri ne da ya yi kaurin suna ta fannin kasancewa maboyar makaman da ‘yan fashi ke amfani da su wajen aikata miyagun ayyuka, shi ya sa Gwamnatin Jihar ya dauki matakin tura jami’an tsaro su kama tare da fatattakar duk wadanda ake zargi da aikata miyagun ayyuka a wurin.