Home Labarai Babu Hannunmu a Kwarmata Sautin Muryoyin Obi, Oyedepo – Ncc

Babu Hannunmu a Kwarmata Sautin Muryoyin Obi, Oyedepo – Ncc

104
0

Hukumar kula da kamfanonin sadawar ta Nijeriya NCC, ta
nesanta kan ta daga zargin da wasu ke yi cewa ta na da hannu
wajen kwarmata sautin muryar da aka ji takararar shugaban
kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi da Bishop David
Oyedepo su na tattaunawa.

A cikin tattaunawar ta wayar tarho dai, an ji Peter Obi ya na neman Bishop Oyedepo ya taimaka masa wajen samun kuri’un Kiristocin yankin kudu maso yammacin Nijeriya, inda ya kwatanta lamarin da Jihadi.

Sai dai yayin da wasu ke zargin ta da kwarmata sautin muryoyin, hukumar NCC ta nesanta kan ta daga lamarin cewa hakan ya saba dokar aiki.

A cikin wata sanarwa ta fitar dauke da sa hannun daraktan yada labarum ta Reuben Muoka, hukumar ta musanta taka wata rawa a fitar da sautin muryoyin, ta na mai cewa kamar yadda dokar sadarwa ta shekara ta 2003 da sauran dokokin kasa su ka tanada, ba ta da ikon ta bi diddigin wata tattaunawar wayar tarho.

Kakakin hukumar NCC ya kara da cewa, hukumar ta kai rahoton wannan zargin da ake yi mata ga jami’an tsaro, domin su gudanar da bincike su kuma dauki mataki idan ya zama dole.

Leave a Reply