Jam’iyyar APC ta musanta korar Mataimakin Shugaban
Majalisar Dattawa Sanata Ovie Omo-Agege kamar yadda
rahotanni su ka bayyana.
Rahotanni dai sun nuna yadda jam’iyyar APC a Jihar Delta ta kori Omo-Agege a cikin wata wasiƙa ɗauke da sa hannun Shugaban jam’iyyar na jihar Ulebor Isaac.
Sai dai wani bangare na jam’iyyar APC a jihar ya yi fatali da korar da aka ce an yi wa sanata Omo-Agege .
A Cikin wata sanarwar da shugabannin bangaren da ke mara wa Omo-Agege baya su ka fitar, sun ce su ne doka ta sani a matsayin shugabannin jam’iyyar APC a jihar ba wancan ɓangaren ba.
You must log in to post a comment.