Gwamnatin jihar Kaduna ta sa ke jaddada cewa dokar hana fita da ta sa a ranar Sallah ta na nan daram.
Kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an ba hukumomin tsaro damar tabbatar da dokar a ranaku da ba Laraba da Alhamin ba.
Bayanin hakan na zuwa ne jim kadan bayan, gwamnatin jihar ta kammala taron majalisar tsaro da ta gudanar a fadar gwamnatin jihar, tare da tabbatar da Laraba da Alhamis a matsayin ranakun fita domin siyan kayan abinci.
Sanarwar ta kuma yi kira ga al’umma su bi dokokin da aka tsara sau da kafa, musamman na hana tafiye-tafiye da hana tarukan ibada da na biki ko siyasa, da duk wata hidima.
Gwamnatin jihar kaduna dai, ta ce ta dauki wannan mataki ne domin kare rayukan al’umma, saboda haka ake rokon mutane su yi hakuri da halin da ake ciki domin kare kan su daga duk wata annoba.
You must log in to post a comment.