Home Labaru Ba Zan Yi Mulkin Kama-Karya Ba – Tinubu

Ba Zan Yi Mulkin Kama-Karya Ba – Tinubu

229
0

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin yin
mulkin da ‘yan Nijeriya za su yi na’am da shi ba na kama-
karya ba.

Tinubu ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke jawabi bayan an rantsar da shi a matsayin Shugaban Nijeriya na 16, a dandalin taro na Eagle Square da ke Abuja.

Ya ce za su rika tuntuba tare da jin ra’ayin jama’a, amma ba za su taba yi masu mulkin kama-karya ba, don haka za su rika sauraron kowa kuma ba za su taba kaskantar da wani saboda ya na da ra’ayi sabanin na su ba.

Sabon shugaban kasar, ya ce sun zo ne su magance kalubalen Nijeriya su warkar da shi, ba wai su fama mata ciwo ba.

Leave a Reply