Home Labaru Ba Zan Amince Da Cin Mutunci Da Yi Mani Zagon Kasa Ba...

Ba Zan Amince Da Cin Mutunci Da Yi Mani Zagon Kasa Ba – Shugaban Npa, Bello Koko

283
0

Shugaban Hukumar Tashoshin Jirage Ruwan Nijeriya NPA,
Mohammed Bello Koko, ya ce wasu mutane sun sha alwashin
bata ma shi suna tare da yi masa zagon kasa, amma ya tsaya a
kan ganin bai amince da hakan ya faru ba.

Ya ce wasu mutane da ba a san ko su wanene ba, su na fakewa da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adam, su na yi ma shi zagon kasa ta hanyar amfani da kafafen yada labarai na yanar gizo domin cimma mummunan burin su na yi ma shi zagon kasa.

Bello Koko, ya ce ganin sun kasa cimma burin su na bata ma shi suna da mutunci, yanzu kuma sun sake rungumar mummunan shirin ganin sun kai ma shi hari da kuma iyalan sa.

Ya ce a duk shekarun da ya yi na aiki a banki da bangaren aikin gwamnati, har yanzu ba a taba samun shi da wani laifin aikata ba daidai ba a wata kotu.

Koko ya kara da cewa, ya na da yakinin cewa, mutuncin shi da aiki tukuru a fagen aikin gwamnati ya sa Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar daukaka girman sa daga Babban Darakta a banagaren harkokin kudi zuwa shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya NPA.

Leave a Reply