Home Labaru Ganduje Ya Mayar Da Martani Kan Bukatar Ya Bayyana a Gaban Hukumar...

Ganduje Ya Mayar Da Martani Kan Bukatar Ya Bayyana a Gaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

66
0

Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya
maida martani a kan sammacin da hukumar yaki da rashawa
da kula da korafin jama’a ta jihar ta ce ta aike masa, domin ya
bayyana a gaban ta ya bada bahasi a kan bidiyon da ake zargin
ya nuna ya na karbar cin hancin daloli.

Shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado dai ya ce ya sa hannu a kan wata takardar sammaci da aka aike wa Ganduje.

Ya ce a cikin wasikar, hukumar ta bukaci Ganduje ya bayyana a gaban ta a makon gobe, domin bada bahasi a kan faifen bidiyon, biyo bayan binciken da hukamar ta ce ta fara a kan lamarin, inda ya ce sun tabbatar da sahihancin faifen bidiyon.

Sai dai Ganduje ta bakin kwamishinan sa na harkokin raya karkara da ci-gaban al’umma Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya maida martani dangane da lamarin, inda ya ce tun a shekaru biyu zuwa uku da su ka gabata Ganduje ya mika lamarin gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, don haka bai kamata a ce wani ya yi sammaci ya ce ya na bincike a kan lamarin da ke kotu ba.

Leave a Reply