Home Home Ba Za Mu Lamunci Yunƙurin Haifar Da Tarzoma A Adamawa Ba –...

Ba Za Mu Lamunci Yunƙurin Haifar Da Tarzoma A Adamawa Ba – Fintiri

275
0

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi zargin wasu miyagun mutane na daukar nauyin wasu matasa da nufin tayar da tarzoma da haifar da rashin zaman lafiya a jihar.

Fintiri ya ce ingantattun bayanan sirri game da ayyukan wasu matasa da ke shirin kutsawa cikin rumbunan gwamnati da na masu zaman kansu, da nufin su fasa, ya ce gwamnatinsa za ta yi maganin duk wanda ke barazana ga zaman lafiyar jihar, domin bukatar kashin kai.

Cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in yada labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya rabawa manema labarai, ta ce, Gwamnatin jihar ba za ta tsaya tana kallon ‘yan tada zaune da masu daukar nauyinsu su na ingiza jama’a su dauki doka a hannunsu ba.

Sanarwar ta cigaba da cewa, gwamna Fintiri ya yi mamakin dalilin da ya sa mutanen ke kin yin amfani da hanyoyin da doka ta tanada don magance matsalolinsu, maimakon haka su na shirin yin zagon kasa ga zaman lafiyar jihar.

Leave a Reply