Home Home Za Mu Daidaita Farashin Abinci Kafin Watan Ramadan – ‘Yan Kasuwar Kano

Za Mu Daidaita Farashin Abinci Kafin Watan Ramadan – ‘Yan Kasuwar Kano

37
0

‘Yan kasuwa a Jihar Kano sun baiwa mazauna jihar tabbacin daidaita farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi kafin zuwan watan azumin Ramadan.

‘Yan kasuwar sun bayyana haka ne jim kadan bayan wata ganawa da Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar, Muhuyi Magaji Rimin-Gado a jiya Litinin bisa zarginsu da boye kayayyakin abinci don tsammanin ya yi tsada su sayar.

In ba a manta ba, a ranar Lahadin da ta gabata, hukumar ta rufe wasu ma’ajiyar abinci guda goma da a ke zargi da boye kayan abinci iri-iri a kasuwar hatsi ta Dawanau.

Da ya ke zantawa da manema labarai a madadin ‘yan kasuwar bayan ganawa da shugaban hukumar, daya daga cikin manyan dillalan kasuwar Singa, Ibrahim Danyaro, ya ce za su yi aiki kafada da kafada da hukumar domin ganin an daidaita farashin kayayyakin abinci domin a samu saukin farashin don saukaka rayuwa ga al’ummar jihar Kano da sauran mutane.

Leave a Reply