Gwamnatin Nijeriya ta ce ba za ta saida kadarorin ta ga wani kamfanin Burtaniya ba, bayan wani hukuncin kotu ya ce kamfanin na iya kama kadarorin Nijeriya domin fitar da dala bilyan 9.
A farkon wannan wata ne, wata kotu da ke London ta ba kamfanin P&ID damar kama kaddarorin Nijeriya a matsayin diyya, saboda saba wata yarjejeniya da su ka kulla ta samar da iskar gas, sai dai ministan shari’a Abubakar Malami ya ce su na bin matakai domin kalubalantar wannan mataki.
Malami ya shaida wa manema labarai cewa, an kulla yarjejeninyar ne a kan yaudara tsakanin Nijeriya da kamfanin, don haka ba za su amince ba.
Ya ce an kulla yarjejeniyar ne tsakanin kamfanin P&ID da ma’aikatar Albarkatun man fetur ta Nijeriya, inda ya ce ita ma’aikatar ba ta da rijiyar man fetur ko guda a karkashin ta, don haka ba ta da hurumin sanya hannu a yarjejniyar.
Ministan ya kara da cewa, sakamakon kulla yarjejeniyar a kan yaudara, su na da abubuwan da za su nuna wa kotu a Amurka na neman ta yi watsi da batun biyan diyyar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/libertytvnews
Twitter: https://twitter.com/libertytvnews
Instagram: https://instagram.com/libertytvng
Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/libertyradioabuja
Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?
Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.
Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com
You must log in to post a comment.