Home Labaru Ba Mu Za A Rabawa N70b Ba – Ƴan Majalisa

Ba Mu Za A Rabawa N70b Ba – Ƴan Majalisa

90
0

‘Yan majalisar tarayya sun musanta zargin cewa za a raba
masu Naira Biliyan 70 daga cikin Naira Biliyan 819 da su ka
sahale wa shugaban ƙasa.

Da ya ke martani a kan lamarin, Shugaban kwamitin yaɗa labarai na Majalisar Dattawa Sanata Yemi Adaramodu, ya ce ba ‘yan majalisa za a raba wa kudaden ba.

Sanata Adaramodu, ya ce za a yi amfani da kuɗin ne wajen gyara da samar da kayan aiki a ofisoshin ‘yan Majalisar Wakilai da na Majalisar Dattawa.

Ya ce yanzu haka ‘yan majalisa da dama an bar su da saya wa ofisoshin su kujeru da tebura da kayan lantarki bayan sauran gyare-gyaren da su ka yi.

Sanatan ya kara da cewa, babu wani ɗan majalisa da za a ba kuɗin gyaran a hannun sa, hukumar majalisar ce za ta yi amfani da kuɗin wajen gudanar da gyare-gyaren da samar da kayan aiki kai tsaye.

Leave a Reply