Home Labaru Ba Mu Karɓi Kuɗi Ba Kafin Amincewa Da Buƙatar Buhari Ta Ciyo...

Ba Mu Karɓi Kuɗi Ba Kafin Amincewa Da Buƙatar Buhari Ta Ciyo Bashi – ‘Yan Majalisa

1
0

‘Yan Majalisar Wakilai sun musanta zargin karɓar Dala
miliyan 15 daga gwamnatin tarayya kafin su amince da
buƙatar sauya fasalin bashin naira tiriliyan 22 da ta karɓa daga
Babban Bankin Nijeriya CBN.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta Benjamin Kalu ya fitar, Majalisar ta zargin a matsayin maras tushe balle makama.

Benjamin Kalu, ya ce sai da su ka tattaunawa da ɓangaren zartarwa da kuma bin diddigin buƙatar kafin su amince, domin a matsayin su na zaɓaɓɓun wakilai, matakai da ayyukan da su ke gudanarwa domin al’umma ne.

Idan dai ba a manta ba, Majalisa ta dakatar da buƙatar na wani lokaci, saboda shawarar da wasu kwamatoci su ka bada ta a gudanar da cikakken nazari game da aikin tallafa wa al’umma da gwamnatin ta ce za ta yi da kuɗin.