Home Labaru Tsaro Ayyukan Sojin Sama: Najeriya Za Ta Kara Sayo Jiragen Yaki 24

Ayyukan Sojin Sama: Najeriya Za Ta Kara Sayo Jiragen Yaki 24

72
0
Jet-airforce

Gwamnatin Tarayya ta bayar da kwangilar sayo sabbin jiragen yaki guda 24 samfurin Leonardo M-346 domin su shige gaba wajen ayyukan sojin sama a Najeriya.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tabbatar cewa tuni gwamnatin ta amince da sayo jiragen masu injina bibbiyu, kuma an kammala duk abin da ya kamata na kawo rukunin farko da ya kunshi 12 daga cikin jiragen zuwa Najeriya.

Kafar Humangle mai yada labarai ta intanet ce ta nakalto Daraktan Tsaron Rundunar Sojin Sama, Ashibel P. Utsu yana sanar da hakan a ranar Alhamis, yana mai cewa sabbin jiragen na da karfin yaki da leken asiri daga nisan zango daban-daban a sararin samaniya.

Ya bayyana cewa sayo sabbin jiragen na daga cikin matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka a yankurin ta na maye gurbin jiragen yaki kirar Alpha Jet a matsayin jagora a cikin jiragen da Rundunar take amfani da su a fagen daga a halin yanzu.

Daraktan Tsaron ya sanar da hakan ne a bayanan sa kan yunkurin gwamnati na kara yawan jiragen yakin Rundunar, bayan haska wani fim din Rundunar a ranar Alhamis, inda a ciki aka nuna nau’o’in jiragen yakin na M-346.