Ma’aikatar tsaro Aljeriya za ta tura ton 150 na kayan jin ƙai ga Falasɗinawa a Gaza daidai lokacin da ake gargaɗin yiyuwar fuskantar yunwa a can.
Kayayyakin sun haɗa da abinci da madarar jarirai.
Wannan tallafin ya nuna irin goyon bayan da Aljeriya ke da shi ga Falasɗinawa,” in ji ma’aikatar tsaron ƙasar.
Jirgin sojoji ne zai yi jigilar kayan jin ƙan a yau Litinin daga filin jirgin saman soji na Boufarik da ke kusa da Algiers, babban birnin ƙasar zuwa filin jirgin sama na El-Arish na Masar da ke kusa da zirin Gaza.
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, an yi ƙiyasin rabin al’ummar Gaza na fama da yunwa sakamakon watannin da aka shafe ana gwabza yaƙi da Isra’ila.
MDD ta yi hasashen mutane za su fuskanci yunwa a arewacin Gaza tsakanin Maris da Mayu sannan al’ummar Falasɗinu za su faɗa cikin yunwa nan da watan Yuli.