Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku
Abubakar, ya zargi shirin shugaba Tinubu na raba wa
magidanta naira dubu 8 har tsawon watanni shida da yunkuri
karkatar da kudaden gwamnati.
Atiku Abubakar ya yi zargin ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa a kan sadarwa Phrank Shaibu, ya fitar.
Ya ce shirin Tinubu na kashe dala miliyan 800 domin rage radadi ga ‘Yan Nijeriya ba ya da bambanci da irin wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na tallafin Korona, wanda hakan ya tona aisrin wasu ‘yan siyasa na boye abincin da ya kamata a raba wa talakawa.
Atiku Abubakar ya kara da cewa, shirye-shiryen da Buhari ya kirkiro sun kare ne kawai wajen kara maida ‘yan Nijeriya talakawa baya, kamar yadda rahotannin hukumar kiddiga ta kasa su ka bayyana.