Rahotanni daga gidan yarin Kuje da ke birnin Abuja na cewa, an samu wata hatsaniya da ta kai ga rasa ran wani fursuna.
Wasu bayanai sun ce, fursunan ya mutu ne bayan an kasa ba shi kulawar lafiya da ta kamata.
Duk da cewa hukumomin gidan yarin sun tabbatar da mutuwar fursunan, amma sun ce an ba shi kulawar da ta kamata.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gidan yarin Chukwuedo Humphrey ya fitar, gidan yarin bai ce uffan a kan hatsaniyar da aka samu ba.
You must log in to post a comment.