Home Labaru Ilimi ASUU Ta Mayar Da Yajin Aikinta Na Sai Baba Ta Gani 

ASUU Ta Mayar Da Yajin Aikinta Na Sai Baba Ta Gani 

90
0

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU, ta sanar da maida yajin aikin da ta ke yi zuwa na har sai abin da hali ya yi.

Daukar matakin dai, ya biyo bayan taron Kwamitin Zartarwa na Kungiyar da aka yi, duk da ya ke ba ta yi cikakken bayani a kan sake tsawaita yajin aikin ba.

Tun ranar 14 ga watan Fabrairu ne, kungiyar ta sanar da tsunduma yajin aikin, bayan ta zargi Gwamnatin Tarayya da kin mutunta yarjejeniyar su tun ta shekara ta 2009.

A baya dai Minista a Ma’aikatar Kwadago Festus Keyamo, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta dakatar da ayyukan ta domin sauraren bukatun kungiyar ba.

Ministan ya ce, Gwamnati ta yi iya bakin kokarin ta, inda ya bukaci iyayen dalibai su nemi malaman su koma makaranta.

Tun fara yajin aikin dai, akalla kungiyoyi daban-daban ne suka yi yunkurin shiga tsakani, amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.