Home Home Assha: Kotu Ta Tuɓe ‘Yan Majalisar Jihar Cross Rivers 20 Da Su...

Assha: Kotu Ta Tuɓe ‘Yan Majalisar Jihar Cross Rivers 20 Da Su Ka Sauya Sheƙa

115
0
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta kori ‘yan majalisar dokoki na jihar Cross River 20 da su ka sauya sheƙa.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta kori ‘yan majalisar dokoki na jihar Cross River 20 da su ka sauya sheƙa.

Jam’iyyar PDP ce ta shigar da ƙarar ‘yan majalisar bisa sauya shekar da su ka yi zuwa jam’iyyar APC.

Yayin zartar da hukuncin, Alƙalin kotun ya ce, ‘yan majalisar su bar kujerun su, bayan sun yi watsi da jam’iyyar da ta ɗauki nauyin su har su ka samu muƙaman da su ke a kai.

Sai dai ‘yan majalisar su na da damar ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin kotun.