Home Labaru Askarawa Sun Kama Mabarata a Makka Da Kusa Da Ka’Aba

Askarawa Sun Kama Mabarata a Makka Da Kusa Da Ka’Aba

308
0

Jami’an tsaron Saudiyya da ke birnin Makkah, sun kama wasu mazauna birnin da wasu biyu da ke bara kusa da masallacin Ka’aba.

Hukumomin sun ce, sun kama wani dan kasar Indiya saboda an kama shi ya na kokarin karkatar da hankulan masu ibada domin su ba shi kudi, sannan sun kama wani dan asalin kasar Moroko da ya ke bara a jikin wata kofar shiga masallacin Ka’aba.

Akwai kuma wani dan kasar Yemen da ya ke amfani da sandunan guragu domin yaudarar masu ibada cewa shi mai nakasa ne.

Haka kuma, an kama wani mutum da ke tura dan sa ya yi bara ta hanyar sa shi a kan keken guragu, bayan bincike ya tabbatar da cewa dan na sa kalau ya ke.

Hukumar kula da tsaron al’umma ta Saudiyya ta sanar cewa, duk wanda aka kama ya na bara, ko kuma wanda ya tura wani ya yi bara, zai shafe kusan shekara guda ya na zaman gidan kaso ko ya biya tarar Riyal dubu 100 ko kuma biyun.

Leave a Reply