Home Home APC Za Ta Binciki Zargin Yin Zagon Kasa Da Goje Ya Yi...

APC Za Ta Binciki Zargin Yin Zagon Kasa Da Goje Ya Yi Wa Jam’iyyar A Zaben 2023

140
0

Jam’iyyar APC reshen jihar Gombe, ta kafa kwamitin da zai binciki zargin yi wa ɗan takarar ta yankan baya a zaɓen da ya gabata na jihar Gombe.

Shugaban jam’iyyar na gundumar Keshere Tanimu Abdullahi, ya ce an kafa kwamitin ne bisa zargin da aka samu cewa, sanata Danjuma Goje ya umarci magoya bayan sa su zaɓi wani ɗan takara da ba na jam’iyyar APC ba.

Ya ce dalilin gano cewa akwai makarkashiyar da Danjuma Goje ya kulla tare da magoya bayan sa na yi wa wani ɗan takara da ba na jam’iyyar APC ba aiki, ya sa aka kafa kwamiti domin a gudanar da bincike.

Tanimu Abdullahi, ya ce ba zai yiwu a zuba wa Danjuma Goje ido ya rika yin abin da ya ga dama ba, bayan a jam’iyyar APC ne ya ke cin moriyar siyasar sa, don haka an ba kwamitin wa’adin makonni biyu ya mika rahoton aikin da ya yi.

Leave a Reply