Home Labaru Kiwon Lafiya Annobar Kwalara: Mutum Biyu Sun Mutu A Katsina

Annobar Kwalara: Mutum Biyu Sun Mutu A Katsina

27
0
suspected cholera patients in the hospital
suspected cholera patients in the hospital

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutum biyu sakamakon bullar cutar kwalara da ta zama annoba a Najeriya.

Hukumomin lafiya na jihar sun ce sun dauki matakan gaggawa na dakile yaduwar cutar inda yanzu mutum 118 suka harbu a jihar.

Kwamishinan lafiya ya shaida cewa cikin matakan da suka dauka shi ne na samar da magungunan da suka kamata.

A cewarsa, kananan hukumomin da aka yi asarar rayukan sune Dutsinma da kuma Katsina,

yana mai cewa cutar ta fi kamari a karamar hukumar Kusada inda a wajen kadai aka samu mutum 62 da suka kamu da cutar ta amai da gudawa.

Kwamishinan ya ce babban aikin da ke gaban su a yanzu shi ne na dakile bazuwar cutar

inda ya nuna cewa ana wayar da kan mutane game da muhimmancin tsaftace muhallan su domin kare kan su daga kamuwa da cutar ta amai da gudawa.

Leave a Reply