Home Labaru Kiwon Lafiya Annobar Korona: Shugaba Buhari Ya Ce Gwamnoni Su Tabbata Al’ummar Su Na...

Annobar Korona: Shugaba Buhari Ya Ce Gwamnoni Su Tabbata Al’ummar Su Na Sanya Takunkumin Rufe Fuska

284
0
Majalisar Dattawa Ta Amince Wa Buhari Cin Bashin Naira Biliyan 850
Majalisar Dattawa Ta Amince Wa Buhari Cin Bashin Naira Biliyan 850

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya hori gwamnoni su tabbata suna tilasta sanya takunkumin rufe fuska a tsakanin al’ummar su a wani mataki na dakile yaduwar annobar korona.

Gargadin shugaban kasan ya zo ne bayan karbar rahoto daga kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona wanda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ke jagoran ta.

Sai dai a yayin mika wa shugaban kasa rahoton, sakataren gwamnatin ya ce ana samun cigaba a fagen yaki da cutar korona da ake yi a fadin kasa.

Boss Mustapha, ya ce zasu sanar da matakin da cutar take nan ba dadewa tare da sanar da mataki na gaba za a dauka.