Home Coronavirus Annoba: Cutar Korona Ta Kashe Ƙarin Mutum Takwas A Najeriya

Annoba: Cutar Korona Ta Kashe Ƙarin Mutum Takwas A Najeriya

101
0
Covid-19: Mutane 23 Sunsake Kamuwa A Jihar Kano, Jimilla 59
Covid-19: Mutane 23 Sunsake Kamuwa A Jihar Kano, Jimilla 59


Ƙarin mutum 590 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya cikin awa 24 da suka gabata, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar.

Kazalika, rahoton na NCDC ya nuna cewa cutar ta halaka ƙarin mutum takwas a ranar Juma’ar.

Rahoton ya ce mutanen da suka kamun sun fito ne daga jiha 18 na faɗin ƙasar. Su ne:

Lagos-308, Akwa Ibom-54, Katsina-40, Oyo-39, Rivers-26, Niger-23, Gombe-19, Ogun-16, Ekiti-15, FCT-10, Nasarawa-10, Delta-9, Bayelsa-5, Plateau-5, Imo-4, Ebonyi-3, Jigawa-3, Kano-1

Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 173,411 ne uska harbu da cutar, 2,149 daga cikinsu sun rasu yayin da aka sallami 164,978 bayan sun warke.