Home Labaru Kiwon Lafiya Annoba: Baƙuwar Cuta Ta Kashe Sama Da Mutane 50 A Iyakar Kogi...

Annoba: Baƙuwar Cuta Ta Kashe Sama Da Mutane 50 A Iyakar Kogi Da Enugu

338
0

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kogi Saka Audu, ya ce waɗanda suka mutu sakamakon wata baƙuwar cuta a Jihar Enugu ne da ke maƙwaftaka da jihar sa.

Yayin hirar sa da manema labarai, kwamishinan ya ce mutane 46 ne su ka mutu, ba 50 ba kamar yadda rahotanni su ka ce da farko.

Majalisar Dokoki ta jihar Kogi dai ta ce mutane 50 ne su ka mutu sakamakon bullar wata baƙuwar cuta a jihar.

Ɗan majalisa Anthony Ujah mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Olamaboro ne ya gabatar da ƙudiri a gaban majalisar, inda ya nemi agajin gaugawa daga gwamnatin tarayya da ta jihar.

Ya ce cutar wadda ba a san irin ta ba, ta na zuwa da alamun ciwon kai da jan idanu da rashin jin yunwa da kasa yin fitsari ko bayan gida da farfaɗiya da kuma kisa.

Mista Ujah, ya ce mazauna yankin Etteh a Olamaboro sun shiga ɗimuwa biyo bayan ɓarkewar cutar, wadda ya ce har yanzu ba a san abin da ke haddasa ta ba, kuma waɗanda su ka kamu su na mutuwa ne a cikin mako guda.