Ƙungiyoyin fararen hula a jihar Edo, sun gudanar da zanga-zanga a birnin Benin domin nuna adawa da karin farashin man fetur da aka yi baya-bayan nan.
Rahotanni sun ce, masu zanga-zangar sun bi ta wasu manyan tituna su na Allah-wadai da karin da kuma tsadar rayuwa a Nijeriya.
Sun ce abin ya na ci masu tuwo a kwarya, inda su ka soki matakin karin farashin man fetur yayin da ake fama da tsantsar talauci a Nijeriya.
Masu zanga-zangar dai su na dauke ne da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban, sun kuma yi watsi da shirin tallafin Naira dubu 8 da Gwamnatin Tarayya ke shirin yi bayan cire tallafin man fetur.