Wasu manyan kungiyoyi sun yi kira ga majalisar dokoki ta tarayya ta janye shirin yin amfani da sama da dala miliyan 56 domin saya wa ‘yan majalisar da wasu jami’ai motocin alfarma guda 465 masu Sulke.
Shugabannin kungiyar sa ido a kan harkokin da su ka shafi majalisun dokoki ta CISLAC da kungiyar SERAP mai sa ido a kan tattalin arziki a Nijeriya, sun ce kudurin tamkar nuna halin ko in kula ne ga yanayin kuncin da talakawan Nijeriya ke ciki.
Kungiyar SERAP, ta kuma ba hukumomin wa’adin mako guda su yi watsi da wannan shirin.
Kungiyoyin biyu, sun kira masu goyon bayan shirin da marasa kishin kasa, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar tashin farashin man fetur da hauhawar farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi.
Babban daraktan kungiyar CISLAC Auwal Musa Rafsanjani, ya ce ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ba a sayo sabbin motocin don ministoci da wasu jami’an gwamnati ba, domin a halin da tattalin arzikin kasa ke ciki sayen motocin ba ya da muhimmanci, duba da cewa ranto kudin ma za a yi.