Sabon Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang, ya ce ya gaji
bashin da ya kai Naira biliyan 200 daga tsohuwar gwamnatin
jihar.
Gwamna Caleb ya bayyana haka ne, a jawabin sa na farko bayan an rantsar da shi a birnin Jos, inda ya ce a halin yanzu jihar Filato ta ci bashin da ya haura Naira biliyan 200, yayin da bangaren kiwon lafiya ke bukatar kulawar gaugawa.
Caleb Mutfwang, ya ce tsarin makarantun jihar Filato ya na bukatar gyara, sannan ababen more rayuwa sun lalace kuma a zahiri kowane bangare ya na bukatar gyaran gaugawa.
Sai dai ya ce duk da dimbin bashin da jihar Filato ke fama da shi ba zai hana su yi wa al’umma aiki yadda ya kamata ba.