Home Labaru Zan Yi Tafiya Da Kowa Da Kowa A Gwamnati Na – Uba...

Zan Yi Tafiya Da Kowa Da Kowa A Gwamnati Na – Uba Sani

1
0

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya tabbatar wa
al’ummar jihar Kaduna cewa gwamnatin shi za ta yi tafiya da
kowa da kowa ba zai nuna bambanci a mulkin sa ba.

Ya ce daya daga cikin abin da zai fi maida hankali a kai shi ne, hadin kan al’ummomin Kaduna da kuma cigaba da ayyukan raya jiha kamar yadda gwamna El-Rufai ya fara.

Gwamna Uba Sani, ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da dauwamammen zaman lafiya da kawo ayyukan ci- gaba a fadin jihar Kaduna.

Ya ce zai dauki tsauraran matakai domin bijiro da ayyukan da za su amfani mutanen Kaduna, ya na mai cewa babban burin shi shi ne jihar Kaduna ta cigaba da samun daukaka da ci- gaba kamar yadda su ka gada daga gwamnatin da ta gabata.

Gwamna Uba Sani, ya ce a jihar Kaduna babu bako babu dan gari, don haka a karkashin mulkin shi duk mazaunin Kaduna dan gari ne ba bako ba, saboda haka zai rugumi kowa kuma zai yi tafiya da kowa domin ci-gaban al’umma.