Home Labaru An Yi Wa Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni Ƙarin Albashi Da Kashi 114

An Yi Wa Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni Ƙarin Albashi Da Kashi 114

224
0

Hukumar Tattarawa da kasafta Kuɗaɗen Shiga ta kasa, ta
amince da ƙarin albashi da kashi 114 cikin 100 ga manyan
jami’an gwamnati.

Waɗanda ƙarin albashin ya shafa kuwa sun haɗa da Shugaban Ƙasa da Mataimakin sa da gwamnoni da ‘yan majalisu da ma’aikatan shari’a da sauran su.

Shugaban hukumar Muhammadu Shehu bisa wakilcin kwamishina a hukumar Rakiya Tanko-Ayuba ya bayyana haka, yayin gabatar da rahoto ga Gwamnan jihar Kebbi Dakta Nasir Idris, inda ya ce ƙarin albashin ya fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairu na shekara ta 2023.

Ya ce matakin ƙarin albashin ya yi daidai da tanadin doka sakin layi na 32 na kashi na 1 a Kundin Tsarin Mulki na shekara ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Leave a Reply