Wata gobara da ta tashi a safiyar ranar Laraba a kasuwar Alaba Rago da ke jihar Legas, ta haddasa asarar miliyoyin naira.
Cikin wata sanarwa da hukumar agajin gaggawa ta jihar ta fitar, ta ce gobarar ta tashi ne cikin dare.
Har kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba.
A cewar, babban sakataren hukumar agaji ta jihar, Dr Femi Oke-Osayintolu, jami’an hukumarsu sun isa kasuwar da wuri bayan kiraye-kirayen wayar da aka rika yi musu daga kasuwar.
Ya ce, koda isar jami’an nasu sun tarar wutar ta fara cin shaguna.
Jami’an hukumar kashe gobara ma sun isa wajen akan lokaci inda basu yi wata-wata ba suka fara kashe wutar a cewar jami’in hukumar agajin.
Ya ce, akwai mutanen da suka yi kokari wajen kashe wutar ma.














































