Home Labaru An Tashi Taron Jam’Iyyar Pdp Lafiya Babu Saɓani

An Tashi Taron Jam’Iyyar Pdp Lafiya Babu Saɓani

12
0
PDF

Jam’iyyar PDP ta amince da ware wa yankin arewa kujerar shugabanci ta kasa, amma kowanne yanki ya na da damar shiga a dama da shi a fagen takarar kujerar shugaban kasa.

Taron dai ya zo da ba-zata, sabanin yadda aka sa ran za a tashi baram-baram tsakanin ‘yan arewa da na kudancin Nijeriya.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar shugabanin ta na jihohi Felix Hassan, ya ce abin da ya faru ba sabon abu ba ne, ya na mai cewa, ganin yadda ‘yan jam’iyyar su ka rika haba-haba da juna sun dauki turbar dinke barakar da ke neman yi masu sakiyar da ba ruwa.

Tsarin Shugabancin jam’iyyar PDP dai ya nanata cewa, matakin rarraba mukaman bai shafi shugabancin kasa ko na majalisa ba.

A karshen watan Oktoba nan ne, jam’iyyar PDP za ta yi babban taron ta na kasa, inda magoya bayan ta za su zabi sabbin shugabanni.