Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba,
ya bada umarnin sauya wa Kakakin rundunar ‘yan sanda na
jihar Katsina CSP Gambo Isah wurin aiki.
An dai sauya Gambo Isah daga helkwatar rundunar ‘yansanda ta jihar Katsina zuwa shiyya ta 14, inda zai cigaba da riƙe muƙamin kakakin ‘yan sanda a jihohin Katsina da Kaduna.
Sauyin wurin aikin dai ya na zuwa ne, bayan da wata ‘yar jarida Ruƙayya Aliyu Jibiya ma’aikaciya a tashar Tambarin Hausa ta fallasa cewa Kakakin rundunar ya ci zarafin ta bayan ya jagoranci wata tawagar ‘yan sanda, inda su ka kama ta da ƙarfi su ka jefa mota tare da fasa mata wayoyi, kafin daga bisani su ka miƙa ta fadar mai martaba Sarkin Katsina, daga nan kuma Sarkin ya bada umarnin a kai ta gidan yari har sai ya neme ta.
Sai dai rahotanni na alaƙanta sauyin da Gambo Isah ya samu a matsayin hukunci bayan taƙaddama ta ɓarke tsakanin shi da Ruƙayya Jibiya.
Wata majiya ta ce, bayanin sauya wa Gambo Isah wurin aikin, ya na ƙunshe ne cikin wata takarda, inda sauyin wurin aikin ya shafi mutane 15, sai dai sunan Gambo Isah ne a farkon takardar, wanda rahotanni su ka ce an sauya ma shi wurin aiki ne saboda cin zarafin ‘yar jarida.
You must log in to post a comment.