Home Labaru An Sanya Dokar Hana Yawo A Karamar Hukumar Mangu, Jihar Filato

An Sanya Dokar Hana Yawo A Karamar Hukumar Mangu, Jihar Filato

105
0

Shugaban riko na karamar hukumar Mangu ta jihar Filato
Markus Artu, ya ce sun dakatar da duk wata zirga-zirgar
motoci da babura in banda jami’an tsaro da wadanda ke
ayyuka na musamman.

An dai sanya dokar ne, biyo bayan wani yamutsi da ya kai ga rasa rai tare da jikkata wasu mutane.

Shugaban kungiyar matasan Mwaghavul Sunday Dankaka Dawap, ya ce zargin da aka yi cewa za a afka ma wadanda ke gudun hijira ne musabbabin tashin rikicin.

A makonnin da su ka gabata dai, an samu munanan hare-hare a karamar hukumar Mangu, wadanda su ka yi sanadiyyar rasa rayukan mutane sama da dari, yayin da dubban mutane su ka yi gudun hijira, lamarin da ya sanya fargaba da zargi a tsakanin mabambantan kabilu da addinai a yankin.

Leave a Reply