Home Labarai An Saki Tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa Da Aka Sace

An Saki Tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa Da Aka Sace

1
0

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun sako
tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa Onje Gye-Wado
bayan sun sace shi a ranar Juma’ar da ta gabata.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar Nasarawa Ramhan Nansel ya tabbatar wa manema labarai haka.

Nansel ya ce tsohon mataimakin gwamnan ya kwashe tsawon kwanaki biyu a hannun ‘yan bindiga, waɗanda su ka sako shi cikin dare bayan matsin lamba daga jami’an ‘yan sanda.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, wasu mahara su ka yi awon- gaba da Gye-Wado, bayan sun shiga gidan sa da ke ƙauyen Gwagi a jihar Nasarawa.