Home Labarai An Kashe Biliyan 2 Da Miliyan 750 Wajen Sayen Kuri’a A Katsina –...

An Kashe Biliyan 2 Da Miliyan 750 Wajen Sayen Kuri’a A Katsina – NNPP

39
0

Jam’iyyar NNPP a jihar Katsina, ta yi zargin yin amfani da kuɗi na fitar hankali wajen sayen kuri’un Daliget a zaɓen fidda gwani na fitar da dan takarar kujerar gwamnan jam’iyyar APC da ya gabata.

Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jihar Katsina Sani Liti ya bayyana haka ne, a wajen wani taron manema labarai da ya gudana a Katsina, inda ya ce kimanin naira biliyan biyu da miliyan ɗari bakwai da hamsin aka yi amfani da su wajen sayen kuri’un Daliget 1,805 a rana guda.

Ya ce idan har gwamnati bata ɗauki mataki a kan wannan lamari ba, to ba a san inda Nijeriya za ta faɗa ba sakamakon muzanta darajar naira da gwamnati ta taimaka aka yi.

Sani Liti ya ƙara da cewa, suna da duk wani bayanin game da kuɗaɗen da aka kashe wajen zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC, wanda mutane tara su ka tsaya takara.

Jam’iyyar NNPP ta kuma yi koken cewa, gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefele ya faɗa harkar siyasa, wanda hakan ya ci karo da dokar ƙasa, don haka ya kamata ya sauka daga aikin sa tun kafin lokaci ya kure masa.