Home Labaru An Kama Wata Mata Da Yunƙurin Sace Yaro Ɗan Shekara 5 A...

An Kama Wata Mata Da Yunƙurin Sace Yaro Ɗan Shekara 5 A Kano

566
0

Wata mata mai matsakaitan shekaru ta shiga hannun hukuma, bayan ta yi yunkurin yin garkuwa da wani dalibi mai shekaru 5 Bashir Jamilu a Jihar Kano, wanda dan karamin aji ne a makarantar firamare ta Ulumuddin da ke unguwar Koki a cikin birnin Kano.

Mahaifiyar dalibin mai suna A’isha Salisu Koki, ta ce ta tura dalibin makaranta ne da misalin karfe 8:30 na safe, inda wata mata ta rike hannun shi ta ce za ta saya ma shi nama da Indomi da madara, amma yaron ya ki yarda ya fashe da kuka, har ta kai ga ya fadi kasa amma matar ta cigaba da jan shi.

Ganin haka ya sa mutane su ka fahimci abin da ke shirin faruwa, inda su ka fara tambayar ta sai tace dan ta ne, amma bayan sun fahimci ba dan ta ba ne sai su ka rufe ta da duka.

Tuni dai an wuce da matar zuwa ofishin binciken sirri, daga bisani aka zarce da ita zuwa bangaren yaki da garkuwa da mutane.

Sai dai Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba ya da bayani a kan lamarin, amma zai gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY