Home Labarai An Kama Fiye Da Mutum 100 Sanadiyyar Rikicin Bayan Zaɓe A Ghana

An Kama Fiye Da Mutum 100 Sanadiyyar Rikicin Bayan Zaɓe A Ghana

107
0
ghana police
ghana police

‘Yan sanda a Ghana sun kama mutum fiye da 100 yawancinsu magoya bayan zababben shugaban kasar John Mahama saboda nuna rashin da’a.

Ana zargin magoya bayan sabon zababben shugaban wadanda ke neman guraben aiki da kai wa cibiyoyin gwamnati hari tare da sata da kuma tayar da tarzoma lamarin da har ya raunata ‘yan sanda da sojoji.

Kazalika magoya bayan sabon shugaban kasar sun kai hari wasu ofisoshin hukumar zabe biyu saboda jan kafar da aka yi kafin sanar da sakamakon zabe.n shugaban kasa dana ‘yan majalisun dokokin da aka yi a ranar Asabar din da ta wuce.

John Mahama, ya yi alawadai da abin da ya faru inda ya yi kira ga shugaba Nana Akufo-Addo da hukumomin tsaro da su dukin matakin da suka dace wajen shawo kan wannan matsala da ta kunno kai.

Shi kuwan mataimakin shugaban na Ghana, wato dan takarar shugaban kasar jam’iyya mai mulkin da ya sha kayi, Bawumiya, kira ya yi ga zababben shugaban kasar da ya ja kunnen magoya bayansa.

Leave a Reply