Kwamitin tsaro da ’yan sanda da sauran hukumomin da haɗin gwiwar Ma’aikatar Noma ta Jihar Legas,
Kwamitin tsaron na haɗaka a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Babban Sufurtandan ’Yan sanda (CSP) Shola Jejeloye,
ya faro samamen ne daga ’yan raguna da ke Unguwar Mangwaro Agege, inda jami’an suka kwashe dabbobi da dama.
CSP Jejeloye ya bayyana wa manema labarai cewa dillalan dabbobin suna gudanar da harkokin su cikin rashin tsafta,
hakan ke janyo haɗari ga masu saye, da masu ababen hawa da ke yawo a titunan da masu dabobbin ke baza hajar su.
dabbobin ba a tsare su ba, cikin sauƙi zasu hau kan titin wanda zai iya haifar da haɗari.
Ya buƙace su kuma su tabbatar suna cinikin su ne a wuraren da hukuma ta amince kaɗai,
akasin haka za a ƙwace dabbobin sa, su zama mallakin gwamnatin jihar.














































