Home Labaru An Gurfanar Da Wadanda Ake Zargi Da Hallaka Yaron Sanata A Gaban...

An Gurfanar Da Wadanda Ake Zargi Da Hallaka Yaron Sanata A Gaban Kotu

115
0

Wadanda ake tuhuma da laifin kisan yaron Sanata Bala Na’Allah marigayi Abdulkarim Na’Allah, sun bayyana a gaban wata babbar kotun jihar Kaduna.

Wadanda ake zargin kuwa sun hada da wani Bashir Mohammed da Nasiru Balarabe da kuma Suleiman Salisu.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce ana zargin mutanen ne da laifin kisa da fashi da makami da taimaka wa wajen aikata laifi.

Wani jami’in gwamnatin jihar Kaduna Dr. Dari Bayero, ya bukaci a dakatar da shari’ar saboda wasu daga cikin wadanda ake zargin ba su je kotu ba, kuma  ba su aika wakilin da zai tsaya masu a kotun ba.

Lauyan da ya tsaya wa Sulaiman Salisu mai suna Avong Emmanuel, ya shaida wa kotun cewa wanda yak e tsaya mawa ba ya da isasshiyar lafiya, don haka ya ke neman a bada belin sa, amma Alkalin bai yi na’am da rokon shi ba, inda ya dage shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Maris 2022.