Home Labaru An Bukaci Kotu Ta Kwace Dala Miliyan 129 Daga Hannun Tsohon Gwamnan...

An Bukaci Kotu Ta Kwace Dala Miliyan 129 Daga Hannun Tsohon Gwamnan Jihar Delta

76
0

Masu gabatar da kara a Birtaniya, sun bukaci kotu ta bada
umurnin kwace kudin da yawan su ya zarce Fam miliyan 100
ko kuma Dala miliyan 129 daga hannun tsohon gwamnan
jihar Delta James Ibori, wanda aka samu da laifin halasta
kudaden haramun a London.

A shekara ta 2011 ne aka tasa keyar Ibori daga birnin Dubai zuwa London domin gurfana a gaban kotu, wadda ta same shi da aikata laifuffukan da su ka hada da sace dukiyar jihar sa da ke yankin Neja Delta.

James Ibori ya amsa tuhume-tuhume 10 da aka yi masa a shekara ta 2012, wadanda su ka hada da zamba cikin aminci da halasta kudaden haramun, lamarin da ya sa kotu ta yanke ma shi hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari.

Bayan kwashe sama da shekaru 10 ana tafka shari’a, yanzu haka an kusa samun hukuncin alkalai na kwace makudan kudaden mallakar tsohon gwamnan.

Rahotanni sun ce, alkalin kotun Crown Court David Tomlison ne ya bada umurnin a karbe dukiyar, kuma tuni lauyoyin bangarorin biyu sun

Leave a Reply