Home Labaru Kasuwanci Man Fetur Da Ake Sha A Najeriya Ya Ragu Da Kashi 35

Man Fetur Da Ake Sha A Najeriya Ya Ragu Da Kashi 35

73
0

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin
man fetur a Nijeriya, ta ce yawan man da ake amfani da shi a
kowace rana ya ragu zuwa lita miliyan 46 da dubu 34
sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Shugaban hukumar Ahmed Farouk ya bayyana haka, yayin taron masu ruwa da tsaki a kan harkokin albarkatun man fetur da iskar gas a Legas.

Ahmed Farouk ya ƙara da cewa, raguwar ta kai kashi 35 cikin 100 idan aka kwatanta da lita miliyan 65 da ake amfani da ita a kowace rana kafin a cire tallafin man.

Ya ce ‘a watannin Janairu da Fabrairu, an sha litar mai miliyan 62 a kowace rana, yayin da aka sha lita miliyan 71 da du bu 400 kowace rana a cikin watan Maris, sai kuma watan Afiru da aka sha lita miliyan 67 da dubu 700 a kowace rana, yayin da a watan Mayu aka sha lita miliyan 49 da rabi a kowace rana, sai kuma watan Yuli da ake shan lita miliyan 46 da dubu 300 a kowace rana’.

Shugaban hukumar, ya kuma gode wa ‘yan kasuwar da su ka nuna sha’awar shigo da man fetur Nijeriya daga kasuwannin duniya, inda ya ce kawo yanzu kamfanoni 56 ne su ka nuna sha’awar shigo da man fetur, yayin da kamfanoni 10 su ka zaku su fara shigo da man.

Leave a Reply