Home Addini An Buƙaci Wasu Maniyyatan Abuja Su Koma Gida

An Buƙaci Wasu Maniyyatan Abuja Su Koma Gida

432
0

Wasu maniyyata aikin hajji sun koka da yadda aka umarci
wasu daga cikin su, su koma gida saboda ba za su samu damar
zuwa aikin hajjin bana ba, duk kuwa da biyan kuɗin aikin
hajjin ta hanyar Adashen-Gata.

Maniyyatan sun ce hakan ya faru ne bayan sun kwashe makonni a sansanin mahajjata na birnin tarayya Abuja.

Daya daga cikin maniyattan da lamarin ya shafa, ta ce ta kwashe sama da tsawon kwanaki goma a sasanin alhazan, amma har yanzu ba ta san makomar su ba sakamakon rashin wani bayani daga bangren mahukunta.

A wani taƙaitacan bayani da darakta a hukumar alhazan Nijeriya Abdullahi Magaji Harɗawa ya yi wa manema labarai, ya ce maniyyatan da ke korafin sun fito ne ba tare da an kira su ba, sai dai ya ce hukumar alhazan ta na ɗaukar mataki.

LEAVE A REPLY