Home Labaru An Bankado Asirin Wasu Ma’Aikatan Hukumar RMAFC Da Yin Kutse A Tsarin...

An Bankado Asirin Wasu Ma’Aikatan Hukumar RMAFC Da Yin Kutse A Tsarin IPPIS

105
0

Shugaban hukumar raba-daidai da kasafta wa gwamnatin
tarayya haraji Dakta Mohammed Bello Shehu, ya tabbatar da
bankado wasu ma’aikatan hukumar bisa zargin su da yin kutse
a cikin tsarin biyan ma’aikata albashi na IPPIS.

Ma’aikatan dai sun yi kutsen ne domin kara wa kan su yawan albashin da gwamnati ke biyan su.

Dakta Bello, ya ce an dakatar da wadanda ake zargin har sai an kammala bincike, ya na mai cewa idan an same su da aikata badakalar da ake zargin su, za a mika su ga mahukuntan da su ka dace domin hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Rahotanni sun ce, an fara zargin badakalar ne yayin da wani ma’aikaci a mataki na 7 a tsarin biyan albashin gwamnati, wanda ya kamata ya karbi naira dubu 60, amma aka biya shi naira dubu 400 daidai da albashin Darakta.

Leave a Reply