Fitattun ‘yan majalisar wakila biyu da ke kan gaba wajen
neman shugabancin majalisar Wakilai Muktar Betara Aliyu da
Yusuf Gagdi, sun janye takarar su tare da mara wa Tajudeen
Abbas baya.
‘Yan majalisar sun nuna goyon bayan Tajuddeen ne bayan sun gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da daddare.
Yusuf Gagdi daga jihar Filato dai ya dade ya na nuna turjiya domin ganin an ba yankin arewa ta tsakiya damar fitar da shugaban majalisar wakilai, yayin da bayanai ke cewa akasarin ‘yan majalisar su na goyon bayan Mukhtar Betara ne kafin wannan lokacin.
Tun farko dai jam’iyyar APC Shugaba Tinubu sun nuna goyon bayan su ga Tajuddeen Abbas daga jihar Kaduna, lamarin da bai yi wa ‘yan majalisa da dama dadi ba, musamman wadanda aka sake zaben su, ciki har da mataimakin shugaban majalisar Ahmed Idris Wase.
A wani sako da mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya wallafa a shafin sa na Twitter, ya ce ‘yan majalisar biyu sun janye takarar ne bayan sun gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.














































