Home Labarai An Ɗora Tubalin Gina Ban-Ɗaki Kusan 2000 A Birnin Abuja

An Ɗora Tubalin Gina Ban-Ɗaki Kusan 2000 A Birnin Abuja

243
0

An ƙaddamar da shirin gina ban-ɗaki akalla dubu biyu a
birnin Abuja domin magance matsalar yin ba-haya a fili.

Hukumomin Nijeriya sun ce, za a ɗauki tsawon shekaru uku
ana gudanar da aikin samar da ban-ɗakin tare da haɗin
gwiwar ƙungiyoyi.

Haka kuma, shirin ya ƙunshi samar da tsaftataccen ruwan
sha, wanda zai taimaka wajen kauda yaɗuwar cututtuka.

Ministan albarkatun ruwa ya bayyana cewa, su na da
niyyar faɗaɗa shirin zuwa jihohi 36 na Nijeriya.

Leave a Reply