Home Labaru Amsa Gayyatar EFCC: Tsohon Shugaban Majalisa Bukola Saraki Ya Koma Gida

Amsa Gayyatar EFCC: Tsohon Shugaban Majalisa Bukola Saraki Ya Koma Gida

193
0

Ofishin watsa labaran tsohon shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki, ya ce ɗan siyasar ya koma gidansa, bayan amsa gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar EFCC ta yi masa.

Haka nan kuma ya karyata wasu rahotanni da jaridun Najeriyar suka ce jami’an hukumar sun tsare shi bayan amsa gayyatar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin Bukola Saraki Yusuph Olaniyonu, ta ce tsohon shugaban majalisar dattawan ya tabbatar wa EFCC cewa a shirye yake ya amsa gayyatarsu a duk lokacin da suka bukaci wani karin haske daga gare shi, yana cewa “Babu wani abu da zai boye musu.”

Da farko dai, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa BBC ranar Asabar cewa sun gayyaci Sanata Saraki ne domin ya amsa wasu tambayoyi game da zarge-zargen cin hanci.

Sai dai bai yi cikakken bayani kan zarge-zargen da suke yi wa tsohon gwamnan jihar ta Kwara ba.

Leave a Reply