Home Labaru Yaki Da ‘Yan Fashi: ‘Yan Sanda A Jihar Imo Sun Kashe ‘Yan...

Yaki Da ‘Yan Fashi: ‘Yan Sanda A Jihar Imo Sun Kashe ‘Yan Mutum Biyu

63
0

Rundunar ‘yan sandan JIhar Imo a kudancin Najeriya ta ce jami’anta sun kashe ‘yan fashi biyu yayin wata musayar wuta a Ƙaramar Hukumar Njaba ranar Asabar.

Kwamishinan “Yan Sandan Imo, Mr Abutu Yaro, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.

Ya ce sun ƙwace bindigar AK-47 ɗaya da kuma wata mota yayin fafatawar.

“Yayin musayar wutar, an lalata ɗaya daga cikin abin hawansu [‘yan fashi] sannan aka kashe biyu daga cikinsu yayin da sauran suka shiga daji a guje,” a cewar sanarwar.

Baya ga AK-47, kazalika an samu wata ƙaramar bindiga ƙirar gida a motar tasu. Sanarwar ta ƙara da cewa ‘yan sanda na ci gaba da bin sawun su.