Home Labaru Kiwon Lafiya Ambaliyar Ruwa: Mutum Bakwai Sun Mutu A Bauchi

Ambaliyar Ruwa: Mutum Bakwai Sun Mutu A Bauchi

224
0
IMG 20240813 WA0021
IMG 20240813 WA0021

Hukumomi a ƙaramar hukumar Shira ta jihar sun tabbatar da mutuwar mutum bakwai sanadiyar ambaliyar da aka samu sakamakon mamakon ruwan sama.

Hukumomin sun ce mamakon ruwan sama da aka shafe sa’oi ana yi a ƙarshen mako ne ya janyo ambaliyar ruwan.

Kantoman ƙaramar hukumar Babangida Ishaq Maliya, ya shaida cewa, ruwan saman da aka yi ya yi sanadin rushewar gidaje da dama ga shafe gonaki.

Ya ce akwai ‘yar shekara 80 da gini ya rufta mata, da ‘yar shekara 15 da kuma yaro wanda duk sun mutu, baya ga waɗannan mutum ukun,

akwai garin Dango, wanda anan ma mace ɗaya ‘yar shekara 15 ta mutu, sai garin ƙaura da namiji guda ya mutu sai kuma garin Kungu da anan ma mace guda ta rasu.

Mazauna ƙauyen Sunkuye, wato ɗaya daga cikin ƙauyukan da aka samu ambaliyar sun ce ruwa ya tafi da wani yaro da har kawo yanzu ba a ganshi ba.

Mutanen garin sun ce yanzu suna cikin jimami da tarabbabin abin da zai iya faruwa da su saboda tsabar ruwan saman da ake kamar da bakin ƙwarya.

Leave a Reply