Home Labarai Masarautar Bauchi Ta Warware Nadin Sarautar Sanata  Shehu Buba

Masarautar Bauchi Ta Warware Nadin Sarautar Sanata  Shehu Buba

303
0
IMG 20240311 WA0003 495x400 1 770x470
IMG 20240311 WA0003 495x400 1 770x470

Sakamakon zargin nuna rashin ladabi ga gwamnan jihar Bauchi, masarautar Bauchi ta kwace sarautar Mujaddadin Bauchi daga wajen Sanatan mazabar Bauchi ta Kudu.

Sanatan, ya kalubalanci gwamnan jihar ta Bauchi Bala Muhammed ne kan sukar manufofin shugaban Najeria Bola Ahmed Tinubu da ya yi.

Rahotanni sun ce sanarwar kwace matsayin sarautar na kunshe ne cikin wasikar da masarautar ta aike wa Sanatan mai dauke da sa-hannun Nasiru Musa.

Wasikar, ta yi bayanin cewa an dauki wannan mataki ne bayan wani taro da majalisar masarautar ta yi karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu,

inda suka tattauna kan kalaman rashin girmamawa da Sanatan ya yi kan gwamnan na jihar Bauchi, inda kuma a karshe majalisar ta amince da kwace matsayin sarautar ta sa.

Majalisar musamman ma, ta zargi Sanatan da cin zarafi tare da nuna rashin girmama gwamnan Jihar Bauchi, lamarin da ta ce ya saba da tanade tanaden tsarin al’adun masarautar.

Idan za a iya tunawa yayin kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kananan hukumomi na jam’iyyar APC  a jihar Bauchi,

Sanata Shehu Buba ya zargi gwamnan Bauchi da karkatar da kayan tallafin da suka hada da shinkafa, da masara da takin zamani da gwamnatin tarayya ta tura wa jihar.

Leave a Reply