Home Labaru Kiwon Lafiya Ambaliyar Ruwa: Gidaje 110 Sun Lalace A Zamfara

Ambaliyar Ruwa: Gidaje 110 Sun Lalace A Zamfara

479
0
Bello Muhammad Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara
Bello Muhammad Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara

Akalla gidaje 110 ne suka ruguje a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, bayan wata ambaliyar ruwa da ta auku a yankin.

Hakan yana kunshe cikin sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar a jiya Juma’a a Gusau, babban birnin jihar.

Sanarwar ta fito ne daga mai ba Gwamnan jihar Bello Matawalle, shawara na musamman kan harkokin jin kai, da kula da bala’o’i da cigaban al’umma, Fa’ika Ahmad.

 A sanarwar Fa’ika, ta bayyana cewa babu asarar rai ko daya da aka samu yayin ambaliyar ruwan, sai dai ta bayyana damuwa kan asarar muhallai da ta janyo wa dubban mutane.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Zurmi tana daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da hukumar kula da yanayi NIMET ta yi hasashen za su fuskanci ambaliyar ruwa a daminar bana.

Leave a Reply